GUDUMMAW AR HAUSAWA GA CIGABAN GARIN GOMBI A JIHAR ADAMAWA
DOI:
https://doi.org/10.62050/d3p0zw93الكلمات المفتاحية:
Gudummawa، Hausawa، cigaba، Gombiالملخص
Wannantakardar mai taken Gudummawar Hausawa ga Cigaban Garin Gombi a Jihar Adamawa, ta yi tsokaci ne kan irin gudummawar da Hausawa suke bayarwa ga garin domin bunƙasarta. Takardar ta yi waiwayen taƙaitaccen tarihin Hausawa da zuwansu garin tare da ɗan abin da ba a rasa ba na daga tarihin garin Gombi. Sannan manufar wannan bincike ita ce bayyanar da wanzuwar Hausawa a garin, da irin gudummawar da suke bayarwa ga ci gabansa tare da cike giɓin da aka bari a fannin ilmi. Sannan an ɗora wannan aiki ne kan ra’in sauyesauyen al’adu (al’umma) wanda Charlse Darwin ya ƙirƙira a shekarar 1958. Wannan ra’i yana bayani ne game da sauyesauye da yake faruwa ga al’umma ko al’adunsu daga wani matsayi zuwa wani, kamar yadda zuwan Hausawa garin Gombi ya taimaka wa ci gaban garin daga matsayinsa na da ya zuwa matsayin da yake a yanzu. Hanyar tattara bayanai kuwa, sun haɗa da yin tambayoyin hira da masana tare da sanya idanu game da rayuwar al'ummomin garin. Daga ƙarshe binciken ya gano irin gudummawar da al'ummar Hausawa suke bayarwa ga ci gaban garin a ɓangarori kamar: yawan jama'a da harshe da tattalin arziƙi da tufafi (sutura) da ilmi da sarauta da siyasa da bukukuwa da abinci da zamantakewa da makamantansu.
التنزيلات
