GUDUMMAW AR HAUSAWA GA CIGABAN GARIN GOMBI A JIHAR ADAMAWA

المؤلفون

  • Isa Umar Al­-Musawi
    Sashen Nazarin Harsuna da Kimiyyar Harshe, Jami'ar Jihar Taraba, Jalingo

الكلمات المفتاحية:

Array، Array، Array، Array

الملخص

Wannantakardar mai taken Gudummawar Hausawa ga Cigaban Garin Gombi a Jihar Adamawa, ta yi tsokaci ne kan irin gudummawar da Hausawa suke bayarwa ga garin domin bunƙasarta. Takardar ta yi waiwayen taƙaitaccen tarihin Hausawa da zuwansu garin tare da ɗan abin da ba a rasa ba na daga tarihin garin Gombi. Sannan manufar wannan bincike ita ce bayyanar da wanzuwar Hausawa a garin, da irin gudummawar da suke bayarwa ga ci gabansa tare da cike giɓin da aka bari a fannin ilmi. Sannan an ɗora wannan aiki ne kan ra’in sauye­sauyen al’adu (al’umma) wanda Charlse Darwin ya ƙirƙira a shekarar 1958. Wannan ra’i yana bayani ne game da sauye­sauye da yake faruwa ga al’umma ko al’adunsu daga wani matsayi zuwa wani, kamar yadda zuwan Hausawa garin Gombi ya taimaka wa ci gaban garin daga matsayinsa na da ya zuwa matsayin da yake a yanzu. Hanyar tattara bayanai kuwa, sun haɗa da yin tambayoyin hira da masana tare da sanya idanu game da rayuwar al'ummomin garin. Daga ƙarshe binciken ya gano irin gudummawar da al'ummar Hausawa suke bayarwa ga ci gaban garin a ɓangarori kamar: yawan jama'a da harshe da tattalin arziƙi da tufafi (sutura) da ilmi da sarauta da siyasa da bukukuwa da abinci da zamantakewa da makamantansu.

Dimensions

منشور

2024-08-31

كيفية الاقتباس

GUDUMMAW AR HAUSAWA GA CIGABAN GARIN GOMBI A JIHAR ADAMAWA. (2024). FULAFIA IAC Book of Proceedings, 205-213. https://doi.org/10.62050/d3p0zw93

إصدار

القسم

Social Science, Arts and Humanities Track

كيفية الاقتباس

GUDUMMAW AR HAUSAWA GA CIGABAN GARIN GOMBI A JIHAR ADAMAWA. (2024). FULAFIA IAC Book of Proceedings, 205-213. https://doi.org/10.62050/d3p0zw93